Real Madrid ce ta fi daraja a Duniya

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid wacce ta lashe kofin zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce kan gaba a jerin kungiyoyin wasa da suka fi daraja da mujallar Forbes kan fitar duk shekara.

Madrid ta kasar Spaniya, kuma mai rike da kofin zakarun Turai, tana da jarin da ya kai dalar Amurka Biliyan 3.44.

Kungiyoyin kwallon kafa uku ne ke kan gaba a jerin kungiyoyin da suka fi arziki a duniya, inda Barcelona ke matsayi na biyu da jarin dala biliyan 3.2 sai Manchester United wacce take da jarin dala biliyan 2.8.

Mujallar Forbes ta fittat da kididdigar ne bayan da ta yi la'akari da tsabar kudin da kulob ke da shi da bashin da ake bin kungiya da hada hadar shiga kallon wasa.

Kungiyar New York Yankees ta Amurka, mai wasan kwallon baseball ke matsayi na hudu da jarin Dala bilyan 2.5.

Dalas Cowboys mai wasan kwallon Amurka nada jarin dala biyan 2.3 a matsayi na biyar.