Luis Suarez ya zama dan Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan na Uraguay ya ciji wasu 'yan wasan kafin Chiellini

Kulob din kwallon kafa na Barcelona ya sayi dan wasan gaban nan Luis Suarez a kan kudi £75 miliyan.

Sai dai kungiyar ta Spaniya ba ta samu damar nuna wa magoya bayanta dan wasan ba, saboda haramcin da aka sa masa na watanni hudu, biyo bayan cizon dan wasan Italiya Giorgio Chiellini.

Amma daraktan wasanni na kulob din na Barcelona, Andoni Zubizarreta ya gaya wa taron manema labarai cewa "Suarez ya zama dan wasan kulob din dari bisa dari."

Sai a watan Nuwamba mai zuwa ne Suarez zai iya buga wa kulob din na Barcelona wasa, ko kuma yin horo da sauran 'yan wasan kulob din, ko da yake idan ya samu nasarar karar da ya daukaka zai iya kafin nan.