Louis van Gaal ya isa Old Trafford

Louis van Gaal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin na fatan dawo da tagomashin kungiyar a bana

Sabon kocin Manchester United Louis van Gaal, ya isa filin atisayen kulob din wato Old Trafford a karon farko.

Kocin dan kasar Holland ya amince ya koma United ne tun a watan Mayu, ya kuma jagoranci kasarsa kaiwa matsayi na uku a gasar cin kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci.

United ta fara daukar horo tun 4 ga watan Yuli, karkashin jagorancin mataimakin koci Ryan Giggs.

Van Gaal zai tattauna da yan jaridu ranar Alhamis.