Fifa: Nigeria ta koma mataki na 34

Nigeria Ranking Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nigeria ta matsa mataki na 3 a jerin kasashen Afirka da suke gaba a taka leda

Nigeria ta gusa zuwa mataki na 34 a jerin kasashen da suka fi iya taka leda a duniya, wanda Fifa ta fitar da sakamakon watan Yuli.

Haka kuma kasar ta koma matsayi na 3 a Afirka, inda Algeriya da Côte d'Ivoire ke mataki na daya dana biyu a jerin kasan da suka fi iya taka leda a Afirka.

Rashin kokarin Ingila a gasar cin kofin duniya, yasa ta koma mattaki na 20, wacce take biye a bayan Bosnia-Hercegovina da Costa Rica da Amurka.

Spain wacce take matsayi na daya a duniya ta koma ta takwas, inda Jamus zakarar kofin duniya ta dare mataki na daya.

Ga jerin kasashe 10 da ke kan gaba a iya taka kwallo a duniya.

1 - Germany 2 - Argentina 3 - Netherlands 4 - Colombia 5 - Belgium 6 - Uruguay 7 - Brazil 8 - Spain 9 - Switzerland 10 - France