Van Gaal ya gana da 'yan jaridu

Louis Van Gaal Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kocin ana sa ran zai dawo da tagomashin United

Sabon kocin Manchester United Louis van Gaal ya bayyana kansa mai martaba mutane da bawa kowa dama, a ganawar da ya yi da 'yan jaridu.

Van Gaal wanda United ta dauko a watan Mayu, ya halarci atisayen kungiyar ranar Talata, inda ake masa lakabi da ba sani ba sabo.

Kocin mai shekaru 62 ya ce "yana bawa kowa damarsa sannan yana martaba mutane a koda yaushe".

"Nasan ina da kwarjini, amma nakan karbi shawarwari da kuma martaba wadanda muke aiki tare" in ji Van Gaal.