Liverpool ta amince da tayin Loic Remy

Loic Remy Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallon ya kwashe kakar bara a Newcastle a aro

Kulob din Liverpool ya cimma yarje-jeniyar dauko dan kwallon QPR mai bugawa Fransa wasa Loic Remy, kan kudi da ya kai fan miliyan takwas.

Dan kwallon mai shekaru 27, ya zura kwallaye 14 a gasar Premier bara inda ya bugawa kulob din Newscatle wasanni a matsayin aro,

Remy, yana cikin tawagar 'yan kwallon Faransa a gasar cin kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci, inda ya buga wasanni biyu a canjin dan kwallo.

Newcastle ta dauki dan wasan ne dai aro daga QPR, lokacin da kulob din ya fadi daga buga gasar Premier a shekarar 2013.