Sunderland ta amince da dauko Borini

Fabio Borini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya taimakawa Sunderland a kakar bara

Kulob din Liverpool ya amince zai sayar da Fabio Borini ga kungiyar Sunderland, kan kudi fan miliyan 14.

Borini, mai shekaru 23, ya kwashe kakar wasa bara a Sunderlan a aro daga Liverpool, inda ya taimakawa kulob din tsallakewa daga barin gasar Premier.

Duk da cimma wannan yarje-jeniyar, Borini ya bugawa Liverpool wasan sada zumunci da Preston North End ranar Asabar, inda Liverpool ta lashe wasan da ci 2-1.

Dan wasan ya zura kwallaye 10 cikin wasannin da ya bugawa Sunderland, sannan ya lashe kyautar matashin dan wasa da yafi fice a kulob din.