NPFL: An dage wasannin zagaye na 2

Nduka-Irabor
Image caption Tun farko an tsaida 20 ga Yuli don ci gaba da gasar

Hukumar gudanar da gasar cin kofin Premier ta Nigeria (LMC) ta sake gusar da ci gaba da wasannin zagaye na biyu zuwa ranar 27 ga watan Yuli.

Dage wasannin ya biyo bayan baiwa kungiyoyin da suke buga gasar kofin kalu bale wato Confederation Cup damar fafatawa a wasan daf dana kusa da karshe ranar laraba.

Tun farko hukumar ta tsaida ranar 20 ga watan Yuli, domin ci gaba da gasar, wacce Kano Pillars ce ke matsayi na daya da maki 34, Nasarawa United da Abia Warriors suke matsayi na 2 dana 3 da maki 31 da kuma 30.

Ga jaddawalin wasannin da za'a fafata ranar 27 ga watan Yuli.

Lobi Stars 16:00 Heartland FC Enugu Rangers vc El-Kanemi Warriors Abia Warriors vs Nasarawa United Akwa United vs Sharks Giwa FC vs Enyimba Warri Wolves vs Kaduna United Sunshine Stars vs Nembe City Bayelsa United vs Crown FC Taraba FC vs Gombe United Dolphins FC vs Kano Pillars