Aspas na daf da komawa Sevilla aro

Iago Aspas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan yana da damar komawa Sevilla idan ya taka rawar gani

Kulob din Sevilla na daf da dauko dan wasan Liverpool Iago Aspas, a aro domin buga mata kwallo har tsawon kakar wasa guda.

Sevilla, tana da damar daukar dan kwallon mai shekaru 26 idan ya taka rawa a kakar bana.

Aspas, ya koma Liverpool ne dai daga Celta Vigo a farkon kafar bara kan kudi fan miliyan bakwai.

Dan kwallon dan Spaniya ya bugawa Liverpool wasanni 15, tara daga ciki a sauyin 'yan wasa inda ya zura kwallo daya kacal a raga.