Evra ya kammala komawa Juventus

Patrice Evra Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Evra ya ce ba zai manta da Manchester United ba

Patrice Evra ya kammala komawa Juventus ta Italiya kan kudi sama da fan miliyan daya daga kulob din Manchester United.

Dan kwallon Faransan mai shekaru 33, ya rattaba hannu a kwantiragin shekaru biyu, wanda hakan ya kawo karshen zamansa a Old Trafford inda ya kwashe shekaru takwas da rabi.

Juventus ce ta bukaci United ta sayar mata da dan kwallon, inda nan da nan Evra ya amince da tayin.

Evra ya koma United ne a watan Janairun 2006 daga kulob din Monaco kan kudi sama da fan miliyan biyar, inda ya buga wa United wasanni 379 ya kuma zura kwallaye 10 a raga.