Man United za ta kara sayo 'yan wasa

Ed Woodward and van gaal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United bata fatan kara kuren da tayi na rashin sayo 'yan wasa a bara

Mataimakin shugaban kulob din Manchester United Ed Woodward, ya bada tabbacin cewa kungiyar za ta fidda kudade domin kara sayo 'yan wasa a makonnan.

Sabon kocin kulob din Louis van Gaal ya dauko mai tsaron baya Luke Shaw da mai wasan tsakiya Ander Herrera, kan kudi fan miliyan 56.

Woodward yayi alkawarin cewa kungiyar baza ta maimaita sakacin da tayi na rashin sayo 'yan wasa a kakar bara ba.

United bata sayo dan kwallo ba, in banda Maroune Fellaini kan kudi fan miliyan 27 daga Everton har aka rufe kasuwar sayen 'yan wasa a lokacin da David Moyes ya maye gurbin Sir Alex Ferguson.