'Ya kamata a bai wa Rooney kyaftin'

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan na fatan zama wanda zai gaji Steven Gerrard

Tsohon kocin Ingila Sven-Goran Eriksson ya ce yakamata a bai wa Wayne Rooney, kyaftin din tawagar Ingila domin ya maye gurbin Steven Gerrard.

Steven Gerrard, mai shekaru 34 ne ya yi ritayar bugawa kasar wasa, dalilin da Erikson ya hango cewa dan kwallon Manchester United Rooney, ya dace ya maye gurbinsa, domin ya buga wasanni 95.

Tsohon kyaftin din Ingila Bryan Robson ya ce, cikin 'yan wasa Rooney da Joe Hart da Gary Cahill ya kamata a zabo wanda zai gaji Gerrard.

Mai tsaron gidan Manchester City Joe Hart mai shekaru 27, ya buga wasanni 43, yayin da dan kwallon Chelsea mai tsaron baya Cahill mai shekaru 28, ya buga wasanni 27.