Ivory Coast za ta dauki sabon koci

Herve Renard Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsohon kocin Zambia da ya lashe kofin Nahiyar Afirka a 2012

Kocin da ya taba lashe kofin Nahiyar Afirka Herve Renard, yana daga cikin masu horaswa biyar da Ivory Coast za ta tantance ta zabi daya domin horas da 'yan wasanta.

Renard, wanda ya lashe kofin Nahiyar Afirka da Zambia a shekarar 2012, yana daga cikin masu zawarcin son horarwa da suka hada da Luis Fernandez da Francis Gillot da Frederic Antonetti da Manuel Jose.

A karshen watan Yuli ne ake sa ran bayyana wanda zai maye gurbin tsohon kocin Sabri Lamouchi, wanda ya kasa taka rawar gani a gasar cin kofin Duniya da Brazil ta karbi bakunci.

Cikin watan Satumba ne, Ivory Coast za ta fara wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka da Morocco za ta karbi bakunci a badi.