Real Madrid ta dauko James Rodriguez

James Rodriguez
Image caption Dan kwallon shi ne ya lashe kyautar kwallon azurfa a gasar kofin Duniya

Kulob din Real Madrid ya dauko dan wasan da ya lashe kwallon zinari a gasar kofin duniya James Rodriguez, daga Monaco dake Faransa.

Dan wasan dan asalin Colombia mai shekaru 23, ya rattaba hannu a kwantiragin shekaru shida don buga wasa a Bernabeu.

Kudin da aka sayo dan kwallon kimanin fan miliyan 63, yasa ya zamo dan wasa na hudu mafi tsada da a ka sayo, bayan Gareth Bale da Cristiano Ronaldo da Luis Suarez.

Rodriguez, ya zura kwallaye shida a raga daga cikin wasanni biyar da ya buga a gasar kofin Duniya da hakan ya kai kasarsa wasan daf da na kusa da karshe.

Daukar dan kwallon da Madrid ta yi, ya zo ne mako guda da kulob din ya dauko Toni Kross daga Bayern Munich.

Rodriguez tsohon dan wasan Porto, ya zura kwallaye 34 a wasannin da ya bugawa Monaco a bara.