Mathieu ya koma Bercelona

Jeremy Mathieu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan shi ne zai maye gurbin Carles Puyol a kulob

Kolub din Bercelona ya sayi dan wasan bayan Valancia Jeremy Mathiew kan kudi fam miliyan 15 da dabu 800.

Mathiew, mai shekaru 30, ya ci wa Faransa kwallaye 2 zai kuma iya taka leda a gefen baya na hagu ko baya ta tsakiya.

Zai maye gurbin tsohon kyaftin Carlos Puyol, wanda ya yi ritaya bayan ya kwashe shekaru 15 yana buga wa kulob din wasa.

A wata sanarwa da Bercelona ta fitar, ta bayyana cewa, an yi musayar dan wasan kan euros miliyan 20, dubu 800 kuma ta yarjejeniya ce da dan wasan.

Mathieu, ya buga wasanni 126 a kakar gasar wasanni 5 a Valancia, ya kuma ci kwallaye 6.