FC Porto ta sayi Yecine Brahimi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Brahimi ya haskaka a Brazil

Dan wasan Algeria, Yacine Brahimi ya sanya hannu a kan kwantiragin shekaru biyar da kungiyar FC Porto ta Portugal daga kulob din Granada.

Dan wasan tsakiyar, haifaffen Faransa mai shekaru 24 ya amince da kwantiragin ta kusan dala miliyan 9.

Yacine Brahimi wanda ya je gasar cin kofin duniya, ya yi rawar gani a gasar bana ta Brazil, inda ya taimaka wa kasarsa kai wa zagaye na biyu.

Brahimi ya sa ragar kwallon Faransa har zuwa matakin kungiyar matasa 'yan kasa da shekaru 21, kafin ya koma don buga wa kasarsa ta asali kwallo.

Karin bayani