'Yan Manchester City sun fice daga fili

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Seko Fofana har yanzu bai bugawa babbar tawaga ba

Kungiyar Manchester City ta 'yan kasa da shekaru 21, ta fice daga wani wasan sada zumunci da aka yi a Croatia sakamakon cin fuska da aka yi wa wani dan wasanta kan bambamci wariya launin fata daga bangaren abokan karawarsu.

An dai hakura da wasan da kulob din ke yi da HNK Rijeka bayan wani tsautsayi da ya faru tsakanin dan wasan tsakiyar Faransa Seko Fofana wanda aka kora bayan wata taho mugama da suka yi ba tare da kwallo ba.

City ta ce, "Hukumar gudanarwar kulob din ce ta yanke hukuncin ficewa daga filin tare da daina cigaba da wasan."

Patrick Viera dan kasar Faransa shi ne kocin kulob din na City.

City ta kara da cewa, "Kulob din na tattaunawa da jami'ansa da masu shirya wasa da kuma hukumar kwallon kafa ta Croatia domin ganin ta tura maganar sama."

Fafona mai shekaru 20, ya koma City daga Lorienta na kasar Faransa a shekarar 2013.

Karin bayani