Donetsk ta sauya filin wasa

Shakhtar Donetsk Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar ta sake filin ne saboda rikicin da ake yi a kasar

Kulob din Shakhtar Donetsk, zai koma buga gasar cin kofin kasar Ukraine arewa da Lviv, mai nisan mil 600, sakamakon tashin hankalin da ke karuwa a Ukraine.

'Yan wasa shida ne suka ki koma wa Donestk, birnin da galiban 'yan tawaye masu goyon bayan, Rasha suka mamaye, bayan da kulob din ya buga wasan sada zumunci ranar Asabar a Faransa.

'Yan wasan da suka ki komawa birnin sun hada da Alex Teixeira da Fred da Dentinho da Douglas Costa da Facundo Ferreyra da Ismaily.

Ana ci gaba da fada a Donetsk, inda dakarun gwamnati suke gusawa daf da sansanin 'yan tawaye masu goyon bayan Rasha.

Shugaban kulob din Rinat Akhmetov ya ce 'yan wasan da suka ki komawa na son fake wa da rikicin ne domin su koma wasa wasu kungiyoyin.