Suarez zai buga Barcelona da Madrid

Louis Suarez
Image caption Barcelona na fatan Suarez zai dawo da tagomashin kulob din

Sabon dan wasan Barcelona, Luis Suarez zai fara buga wa kulob din wasa a karawar da za su yi da Real Madrid ranar 26 ga watan Oktoba.

Suarez, wanda aka sayo daga Liverpool kan kudi fan miliyan 75, an dakatar da shi buga wasa na watanni hudu, bayan da aka same shi da laifin cizon dan kwallon Italiya Giorgio Chiellini a gasar cin kofin Duniya.

An hukunta dan wasan ne ranar 1 da watan Yuli bisa laifin da ya aikata ranar 24 ga watan Yuni, zai dawo kwallo kenan a karawa tsakanin Barcelona da Real Madrid a Bernabeu.

Kungiyoyin biyu za su sake kara wa ne a wasa na biyu na cin kofin La Liga ranar 22 ga watan Maris a shekarar 2015.

Suarez an dakatar da shi buga kwallo da shiga dukkan wata sabga data shafi harkokin Fifa, ba zai yi kuma atisaye da 'yan kulob dinsa ba, sannan bazai halarci harabar filin wasa ba.