Lampard ya koma Amurka kwallo

Frank Lampard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce ba zai manta da kulob din Chelsea ba

Tsohon dan kwallon Chelsea Frank Lampard, ya koma kungiyar kwallon kafa ta New York City kan kwantiragin Shekaru biyu.

Lampard, mai shekaru 36, wanda kwantiraginsa ya kare da Chelsea a kakar bara, ya buga wa kulob din wasanni tsawon shekaru 13.

Dan wasan ya koma Chelsea ne daga West Ham a watan Yulin 2001 kan kwantiragin fan miliyan 11, inda ya buga wa Chelsea wasanni 649 ya zura kwallaye 211 a raga.

Lampard ya ce 'Kulob din New York naga yafi dacewa na koma kwallo kuma na yi farinciki, sannan kungiyar Chelsea na rai na a kullum'.

Sabuwar kungiyar New York City, za ta fara fafatawa a gasar cin kofin Amurka MLS a kakar wasan 2015.