Farah ya janye daga gasar Commonwealth

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Farah a gasar guje-guje a Moscow

Zakaran tseren gudun fanfalaki, Mo Farah ya fasa shiga gasar Commonwealth da ake yi a Glasgow saboda bai murmure daga ciwon da yake fama da shi ba.

Farah mai shekaru 31, ya lashe kyautar zinare a tseren mita 5,000 da 10,000 a gasar Olympics a 2012 kuma an shirya zai shiga tseren a Scotland.

Sai dai ya shafe lokaci mai tsawo yana horo a Zurich amma kuma bai warke ba.

Tawagar Ingila ta ce "Mun dauki hukunci mara dadi na janye shi daga gasar Commonwealth."

Mo Farah ya kasance daya daga cikin 'yan wasan da Ingila take saran zai samu kyautar zinare.

Karin bayani