An yi kutse a wasa da kolub din Isra'ila

Hakkin mallakar hoto PANARAMIC PHOTOSHOP
Image caption Babu wanda ya ji rauni lokacin da lamarin ya auku

Masu zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu sun kawo cikas lokacin wani wasan kwallon kafa da aka shirya tsakanin kulob din Isra'ila Maccaba da Lille na Faransa da za a yi Australia.

Wasan sada zumuncin da aka shirya kafin fara Gasar wasanni a Bischofshofen ya gamu da cikas ne yayin da masu goyon Falasdinawa suka shiga filin wasan dauke da Tutar kasar Falasdinu suna kadata.

Sai dai ga dukkan alamu ba wani wanda ya samu rauni.

Isra'ila ta kai wani harin soji ranar 8 ga watan Yuli, tare da bayyana manufarta na dakatar da kai harin roka daga Gaza.

Jami'ai sun bayyana cewa, an kashe akalla Falasdinawa 649 da sojojin Isra'ila 32 cikin kwanaki 15 da suka shude.

Karin bayani