NFF: An cire Maigari daga mukaminsa

Aminu Maigari
Image caption NFF za ta gudanar da zaben shugabannita cin watan Agusta

Kwamitin gudanarwa na hukumar wasan kwallon kafa a Nigeriya (NFF) ya kori Aminu Maigari daga mukaminsa, bayan kammala taron data gabatar ranar Alhamis.

Kwamatin gudunarwar ya yanke hukunci yanke kauna kan salon jagorancin shugaban na NFF Aminu Maigari.

A wani rahoto da kwamitin ya fitar ya amince da korar Aminu Maigari daga kwamitin Amintattu bisa samunsa da laifin almubazzaranci da rashin iya gudanar da aiki.

Kwamitin ya nada mataimakin shugaban hukumar na farko Chief Mikel Okeke Umeh, ya maye gurbin Aminu Maigari, har zuwa lokacin da za'a zabi sabbin shugabannin hukumar a ranar 26 ga watan Agusta.

A makon jiya ne dai Fifa ta dage dakatarwar da ta yi wa Nigeriya daga shiga harkokin kwallon kafa, bayan da wata kotu a Jos ta gyara hukuncin da ta zartar na sauke mahukuntan hukumar kwallon kafar NFF karkashin jagorancin Aminu Maigari.