Dan Bosnia Besic zai koma Everton

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Besic ya haskaka a gasar da aka yi a Brazil

Everton na dab da kammala sayen dan kwallon Bosnia Muhamed Besic daga kungiyar Ferencvaros.

Besic mai shekaru 21, wanda ya buga dukkannin wasannin uku da kasar Bosnia-Hercegovina ta yi a gasar cin kofin duniya da a kammala a Brazil, zai ya koma Everton na bada jimawa ba.

Kocin Toffees Martinez ya ce, "Ina san gode wa Ferencvaros kan hanyar da ya bi wajen aiwatar da yarjejeniyar, gaskiya sun bada hadin kai."

Besic, ya koma kulob din Hungaria ne a kakar da ta kare daga Stuttgart, sannan ya kuma haskaka a gasar cin kofin duniya duk da ficewar Bosnia da wuri daga gasar.

Shi ne dan wasa na biyu da Martinez ya dauka a wannan bazarar bayan Gareth Barry wanda ya koma kulob din dindindin a karshen zamansa na aro da Manchester City ta ba da shi a kakar bara.

Karin bayani