Arsenal ta sayo Calum Chambers

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Calum Chambers

Arsenal ta sayi dan kwallon Ingila mai shekaru 19, Calum Chambers daga Southampton a kan fan miliyan 16.

Dan shekaru 19, Chambers na buga kwallo a baya ta gefen dama ko kuma ta tsakiya.

Kocin Gunners Arsene Wenger ya ce "Ya nuna kwazo a kakar wasan da ta wuce a gasar Premier."

Arsenal kuma na zawarcin wani dan kwallon Southampton Morgan Schneiderlin.

Chambers ne dan kwallo na hudu da Arsenal ta sayi a wannan bazarar bayan Alexis Sanchez daga Barcelona da Mathieu Debuchy daga Newcastle da kuma David Ospina daga Nice.

Karin bayani