Greizmann na gab da komawa Atletico

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Antione Griezmann ya haskaka a Brazil

Atletico Madrid za ta sayi dan kwallon Real Sociedad Antoine Griezmann bayan an kamalla gwada lafiyarsa.

Dan wasan mai shekaru 23 na cikin tawagar Faransa a gasar cin kofin duniya da aka buga a Brazil inda aka fitar da kasar a zagayen gab da na kusa da karshe.

Sanarwa daga Atletico Madrid ta ce "Matashin dan kwallon Faransan zai sanya hannu a yarjejeniya bayan an gwada lafiyarsa."

Griezmann zai kasance dan wasa na biyu da zai koma Atletico bayan Mario Mandzukic.

Karin bayani