Commonwealth: An dakatar da Amalaha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Laraba Chika za ta san makomarta

Shugaban shirya gasar Commonwealth, Mike Hooper ya sanarda cewar an dakatar da 'yar wasan Nigeria mai daga nauyi Chika Amalaha saboda zargin shan haramtacciyar kwaya mai kara kuzari.

Amalaha ta samu kyautar zinare a ajin nauyin kilogram 53 a bangaren mata.

Gwajin da aka gudanar a kan Amalaha ya nuna cewar ta akwai kwayar amiloride da kuma hydrochlorothiazide a cikin jininta.

A ranar Laraba za a kara gudanar da gwaje-gwaje a kan 'yar wasan.

Karin bayani