Ebola: An dakatar da kwallo a Liberia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ebola ta hallaka mutane fiye da 600 a Afrika

Hukumar kwallon kafa ta kasar Liberia ta dakatar buga gasar kwallon kafa a fadin kasar, a wani kokari da take yi don hana yaduwar cutar Ebola.

Hukumar ta ce wasan kwallon kafa ana yinsa ne ta hanyar haduwar mutane suna gogayya da juna a wuri guda, don haka akwai hadarin harbuwa da cutar Ebola.

Kazalika gwamnatin kasar ta bukaci ma'aikata da su zauna a gidajensu har zuwa lokacin da za a sake kiransu su koma bakin aiki.

An baza 'yan sanda a filin saukar jiragen sama da ke Monrovia don tabbatar da cewa an tattance dukkan fasinjojin da ke shiga da fita.

Karin bayani