Ba zan yi gaggawar sayen 'yan wasa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Van Gaal da mataimakinsa Ryan Giggs

Kocin Manchester United Louis van Gaal ya ce ba zai yi gaggawar sayen karin sabbin 'yan wasa ba a lokacin da suke ci gaba da rangadi a Amurka.

Dan kasar Holland din wanda ya yi amfani da salon wasan 3-4-1-2 a wasanninsa biyu na sada zumunci ya ce har yanzu tawagarsa na bukatar kwaskwarima.

Irin salon wasan kenan da kocin ya yi amfani da shi a gasar cin kofin duniya tare da Netherlands.

Van Gaal ya ce "Bana sayen 'yan wasa domin inbi Yarima asha kida."

Kalubalen da ke gaban kocin shi ne sannin salon da zai dace wajen amfani da manyan 'yan wasansa uku Wayne Rooney, Juan Mata da kuma Robin van Persie.

Karin bayani