Everton ta kammala cinkin Lukaku

Romelu Lukaku
Image caption Lukaku ya fara fice yana dan shekara 16 a Anderlecht a kakar 2009-10, inda ya ci kwallaye 15, suka dauki lig din Belgium

Kungiyar Everton ta kammala sayen Romelu Lukaku dan wasan Belgium, da ke Chelsea amma kuma yake zaman aro a Everton din kan fam miliyan 28 na tsawon shekara biyar.

Lukaku, mai shekaru 21, ya zura kwallaye 16 lokacin da ya buga wa Everton wasannin, matsayin da ya kai kungiyar karewa a mataki na biyar a teburin Premier, sannan ta samu gurbin shiga gasar Europa, wanda rabonta da gasar tun shekaru biyar baya.

Dan kwallon ya koma Chelsea ne dai daga Anderlecht kan kudi fan miliyan 18 a watan Agustan 2011.

Lukaku ya kwashe shekarar kakar wasa ta 2012-13 a kungiyar West Brom a aro, sannan wasanni 15 ya buga wa Chelsea a duk tsawon zamansa a klub din.

Cinikin Lukakun shi ne wanda kungiyar Everton ba ta taba kashe kudi kamarsa ba, kafin nasa na Marouane Fellani ne loacin da ta sayo shi kan fam miliyan 15 daga Standard Liege a 2008.