Toure: Zama daram a Man City

Yaya Toure Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dan wasan yayi korafin cewa City bata girmama shi ba lokacin bikin ranar haihuwarsa

Dan kwallon Manchester City Yaya Toure ya ce zai dade yana bugawa kulob din wasanni har zuwa lokaci mai tsawo.

A bara anyi ta rade-radin cewa dan kwallon mai shekaru 31 dan kasar Ivory Coast baya jin dadin bugawa kulob din wasa.

Mai kula da harkar wasanninsa Dimitry Seluk, ya taba cewa dan kwallon yayi korafin City bata girmama shi ba.

Toure ya fada a shafin intanet na City cewa "Ba yana nufin zai bar kulob din bane, illa ya shiga tsaka mai wuya ne."

Seluk ya shaidawa sashin wasanni na BBC cewa Toure yana bukatar City ta bashi aiki na dindindin ko da ya dena buga tamaula.