Lazio ta dauko Stefan de Vrij

Stefan de Vrij Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya bugawa Netherlands gasar cin kofin Duniya

Kungiyar kwallon kafa ta Lazio ta dauko dan wasan Netherlands Stefan de Vrij daga kulob din Feyenoord.

De Vrij, mai shekaru 22, ya bugawa Netherlands wasanni bakwai data kara a gasar cin kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci.

Dan wasan mai tsaron baya, an yi rade-radin cewa Manchester United zai koma don buga tamaula tare da Louis van Gaal.

De Vrij ya ce "Ya ji dadin komawa Lazio, kuma kulob din ya nuna masa da gaske yana bukatar wasansa, saboda haka zai yiwa kulob din wasa tukuru."