Ezekiel ya koma Al-Arabi a Qatar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Imoh Ezekiel zai samu kudi mai yawa a Qatar

Dan wasan gaba na Nigeria, Imoh Ezekiel ya koma kungiyar Al-Arabi SC ta Qatar daga kulob dinsa na Standard Liege.

Ezekiel mai shekaru 20 ya bar kungiyarsa ta Belgium ne bayan shafe shekaru biyu yana murza leda.

Rahotanni na cewa dan wasan na Nigeria zai kasance mafi karbar kudi a kungiyar ta Al-rabi, inda za a dunga bashi kimanin dala miliyan 3.8 a duk shekara.

Ana ganin cewar kungiyar ta kasar Qatar ta sayi dan wasan wanda ya zura kwallaye 32 a wasanni 91 da ya buga wa Standard Leige, a kan dala miliyan 10.8