Za a dunga sa ido kan 'yan wasan United

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Van Gaal zai iya fuskantar matsin lamba a United

Kulob din Manchester United ya kawo wata kyamara kirar 'Hi-tech' wadda sabon kocin ta Van Gaal zai rinka amfani da ita wajen sa ido kan 'yan wasa.

Dan wasan baya Jonny Evans ya ce, "Yin nazari ta hanyar amfani da faifan bidiyo na daga cikin dalilan da suka sa kulob din ya tafi rangadi Amurka."

Ya ce, "Sun kashe dubannai kan kyamarar kuma kadan daga cikin 'yan wasan sun ganta a fili. Muna da na'urar da zai rinka amfani da ita wajen sa ido kan mu yayin da muke filin wasa."

Tsohon kocin Netherlands, Van Gaal ya maye gurbin David Moyes da aka kora bayan kasa taka rawara gani a kakar wasan da ta wuce.

Karin bayani