AFCON: Lesotho ta yiwa Kenya kancal

Kenya vs Lesotho
Image caption Lesotho ta yi waje da Kenya a neman gurbin shiga gasar kofin Nahiyar Afirka

An zare Kenya daga kasashen dake neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka, bayan da suka tashi wasa babu ci da Lesotho ranar Lahadi.

Kenya ce ta mamaye kusan dukkan wasan duk da amfini da 'yan wasan Southampton Victor Wanyama da kuma McDonald Mariga dake wasa a Italiya da suka yi.

Lesotho ta sami kaiwa wasan gaba, bayan da Bushi Moletsane ya zurawa Kenya kwallo a karawar farko da su ka yi a wasan farko mako biyu baya.

Sauran wasan da aka kara Mozambique ta doke Tanzania da ci 2-1, ta kuma kai zagayen gaba da yawan kwallaye 4-3 haduwa biyu da suka yi.

Sama da kasashe 28 ne za'a raba zuwa rukunnai 7 a Satumba da Oktoba da Nuwamba, domin tantance kasashen da za su hadu da Morocco mai masaukin bakin gasar cin kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2015.