Liverpool ta doke AC Milan 2-0

Liverpool vs AC Milan Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Liverpoo ta lashe wasanni biyu tayi rashin nasarar wasa daya a Amurka

Kungiyar Liverpool ta doke AC Milan da ci biyu da nema a Amurka a wasannin cin kofin International Champions cup a Charlotte.

Joe Allen ne na Liverpool ya zura kwallo a ragar Milan bayan minti na 17 da fara wasa, kafin daga baya Suso ya kara kwallo ta biyu daf a tashi wasa.

Ranar Litinin Liverpool za ta kara da Manchester United a wasan karshe a Miami.

Daniel Sturridge bai buga karawar ba sakamakon jinyar rauni da yake yi, inda ya koma gida domin kara duba raunin da ya yi.

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce yana sa ran Sturridge zai samu sauki kafin wasan sada zumunci da za su kara da Borussia Dortmund ranar 10 ga watan Agusta.

Liverpool tayi rashin nasara a hannun Roma daga baya ta doke Olympiakos ta kuma lashe Manchester City a wasannin data buga a Amurka.