Lampard zai koma Manchester City aro

Frank Lampard Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan zai bugawa City gasar Premier da kofin zakarun Turai

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini, ya ce sabon dan wasan New York City Frank Lampard zai koma City aro har zuwa watan Janairu.

Pellegrini, ya shaidawa 'yan jaridu cewa daga ranar Laraba Lampard zai fara wasa da kungiyar City har zuwa watanni biyar.

Lampard, mai shekaru 36, ya koma New York City ne a watan jiya, bayan da ya rattaba kwantiragin shekaru biyu, lokacin da kwangilarsa ta kare da Chelsea a bara.

Kulob din New York City da kungiyar wasan baseball ta New York Yankees, suna daga cikin mamallakan Manchester City kuma kakar wasansu sai a watan Maris 2015 za su fara tamaula.

Tuni Manchester City ta shirya yin rijistar dan kwallon Ingila a gasar cin kofin Premier da kuma gasar cin kofin zakarun Turai.