Kocin Zambia Beaumelle ya ajiye aiki

Patrice Beaumelle Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Beamelle ya dade yana aiki tara da Herve Renard

Patrice Beaumelle ya ajiye aikin horas da tawagar 'yan kwallon Zambia watanni tara kacal da fara kocin Chipolopolo.

Ana tunanin zai koma mataimakin Herve Renard, wanda ya karbi ragamar horas da tawagar Ivory Coast a makon jiya.

Beaumelle ya yi wa Renard mataimaki, lokacin da suka horas da Zambiya, daga baya ya maye gurbinsa a watan Oktoban bara bayan da Herve ya yi ritaya.

Tun farko Renard da Beaumelle sun horas da Angola da kulob din USMA na Algeria kafin su karbi ragamar kocin tawagar Zambia.

Haka kuma sun jagoranci Zambia lashe kofin nahiyar Afirka a shekarar 2012 da Equatorial Guinea da Gabon suka karbi bakunci.