Romeu ya koma Stuttgart wasa aro

Oriol Romeu Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan zai buga kakar wasa guda a Stuttgard ne

Dan kwallon Chelsea Oriol Romeu ya koma kulob din Stuttgart domin ci gaba da buga wasanni aro har tsawon karshen kakar bana.

Dan kwallon Spaniya ya rattaba kwantiragi ne dai da Blues a watan Yuli, inda ya ci gaba da kwallo a Valencia aro.

Romeu, mai shekaru 22 da haihuwa, yana daga cikin 'yan wasan Chelsea da suke buga wasannin atisaye a bana, kafin ya koma Jamus wasa.

Ya koma Stamford Bridge ne daga Barcelona a shekarar 201, inda ya bugawa kungiyar wasanni 33.