'Zargin Fifa na cin hanci bata suna ne'

Gary Lineker Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tsohon dan kwallon Ingila Gary Lineker

Tsohon dan wasan gaban Ingila Gary Lineker, ya ce zargin da Fifa ke yi na cin hanci bata suna ne ya kuma kaluballanci rawar da shugaban Fifa ke takawa Sepp Blatter.

Fifa dai na zargin cin hanci ne dangane da baiwa kasar Qatar damar karbar bakuncin gudanar da Gasar cin kofin duniya a 2022.

Lineker ya ce, "Abubuwan Fifa za su saka rashin lafiya, cin hanci da rashawa a tsakanin manyan shugabanninta abun takaici ne."

Ya kuma kara da cewa, "Sepp Blatter ya gudanar da mulkin kama-karya na tsawon lokaci, inda ya kawo abubuwa ma su yawa marasa kyau."

Sai dai kwamatin da ya jagoranci mika bukatar a baiwa Qatar damar karbar bakuncin Gasar ya nisanta kansa kan wannan zargi.