Rodwell na daf da komawa Sunderland

Jack Rodwell Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya yi fama da jinyar rauni a Man City

Kungiyar Sunderland na tattaunawa da takwararta ta Manchester City a kokarin daukar dan kwallonta mai wasan tsakiya Jack Rodwell.

Tuni dan wasan mai shekaru 23, ya isa Wearside don cimma matsaya da kuma duba lafiyarsa.

Rahotanni na cewa Sunderland na son sayen dan kwallon kan kudi fan miliyan 10.

Rodwell ya koma City ne daga Everton kan kudi fan Miliyan 12 a shekarar 2012, ya buga wasanni 25, inda ya yi fama da jinyar rauni.