Real Madrid ta dauko gola Navas

Keylor Navas Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Golan ya zama dan kwallo na uku da Madrid ta dauko

Kulob din Real Madrid ya dauko golan Costa Rica Keylor Navas daga kungiyar Levante kan kwantirangin shekaru shida.

Navas, mai shekaru 27 da haihuwa, ya taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da Brazil ta karbi bakunci, inda kasarsa ta kai wasan daf da na kusa da karshe.

An tabbatar da cewa Levante ta yadda da tayin sama da fan miliyan bakwai ne dake yarjejeniyar dan wasan idan zai bar kulob din.

Madrid za ta gabatar da Navas ga magoya bayanta ranar Talata a Bernabeu bayan an duba lafiyarsa.

Golan shi ne dan wasa na uku da Madrid ta dauko a bana bayan Toni Kross da James Rodriguez.

Navas zai fafata da Iker Casillas da Diego Lopez a gurbin golan da zai kamawa Madrid kwallo a gasar wasannin bana.