Roy Carroll ya koma Notts County

Roy Carroll Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon golan Manchester United Roy Carroll

Tsohon dan kwallon Manchester United Roy Carroll ya koma kulob din Notts County a kwantiragin shekara daya, bayan da ya bar Olympiakos.

Dan wasan Ireland ta Arewa mai shekaru 36 da haihuwa zai maye gurbin Bartosz Bialkowski wanda ya koma kulob din Ipswich.

Carroll ya lashe kofuna uku da kungiyar Olympiakos tun lokacin da ya koma kulob din.

Yana kuma da kwarewar buga gasar cin kofin zakarun Turai da Olympiakos da kuma Manchester United inda ya buga kwallo tsawon shekaru hudu a can.

Carroll ya bugawa Derby County da West Ham wasa a gasar cin kofin Premier da Rangers ta Scottland da Odense ta Denmark da OFI Crete kafin ya koma Olympiakos.