Renard zai dawo da martabar Ivory Coast

Herve Renard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin ya ce zai dawo da tagomashin Ivory Coast

Sabon kocin tawagar Ivory Coast Herve Renard, ya tsara yadda zai dawo da tagomashin kasar a gasar wasan kwallon kafa.

Kocin dan kasar Faransa, an nada shi sabon mai horas da 'yan wasan kasar ne ranar 31 ga watan Yuli da ya wuce, wanda ya gaji tsofaffin 'yan wasa da suke bugawa kasar wasa.

Kocin ya ce "Zai dawo da martabar kungiyar , tare da sauya wasu daga cikin 'yan wasa", wanda kasar za ta fara wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka a watan gobe.

"Ba duka 'yan wasa zan sauya ba, domin akwai kalubale a gabanmu a watan Satumba, amma zan kawo sabbin jini cikin tawagar 'yan wasan".

Ivory Coast za ta fara wasanta na farko a rukuni, a neman gurbin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka da Saliyo a ranar 6 ga watan Satumba a birnin Abidjan.