Jonathan ya yabi tawagar C'wealth

Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban zai karrama 'yan wasan da suka yi fice a Abuja

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan, ya yaba kwazon tawagar kasar a gasar wasannin Commonwealth da birnin Glasgow na Scotland ya karbi bakunci.

Musamman, Shugaba Jonathan ya yabawa Blessing Okagbare, wacce ta mamaye tseren gudu na mata da kuma 'yan wasan da suka lashe lambobin yabo a kasar.

Shugaban ya jaddada kokarin tawagar kasar wacce ta kare a matsayi na takwas daga cikin kasashe 71, da cewa ya nuna yadda 'yan wasan suka sa kwazo da sadaukar da kai da kishin kasa.

Shugaba Jonathan ya tabbatarwa tawagar 'yan wasan cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da marawa 'yan wasa baya da nufin yin fice a duniya don bunkasa kasar.

Shugaban zai karbi bakuncin tawagar 'yan wasan da masu horas dasu nan gaba da nufin girmamasu a Abuja.