Sunderland ta dauko Jack Rodwell

Jack Rodwell
Image caption Dan wasan ya yi fama da jinyar Rauni a Man City

Kungiyar Sunderland ta dauko dan wasan Manchester City Jack Rodwell, mai wasan tsakiya kan kwantiragin shekaru biyar.

Dan kwallon Ingila mai shekaru 23, ba a bayyana kudin da ya koma kulob dinba, amma ana hasashen zai kai fan miliyan 10.

Rodwell ya koma City ne daga Everton kan kudi fan Miliyan 12 a shekarar 2012, ya buga wasanni 25.

Dan wasan yasha fama da jinyar rauni abinda yasa bai samu damar buga wasanni ba akai-akai a Manchester City.