Man United ta lallasa Liverpool

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Manchester United suna murnar cin kwallo.

Manchester United ta kammala wasannin ta na rangadi a Amurka cikin nasara ba tare da an jefa mata kwallo ba, inda ta lallasa abokiyar hamayyarta Liverpool da ci 3-1.

Bugun fenariti da Steven Gerrard ya samu ne ya fara bai wa Liverpool nasara, amma Wayne Rooney da Juan Mata da kuma Jesse Lingard suka mai da martani inda kowannen su ya ci wa Manchester United kwallo daya.

Akalla 'yan kallo sama da mutum 50,000 ne suka hallara a filin wasa na Sun life da ke Miami Dolphins, domin kallon wasan karshe na zakarun.

Sabon kocin Manchester United, Louis Van Gaal, cewa ya yi "Abin sha'awa ne ga magoya bayan mu a Amurka da kuma gida ganin irin yadda muka lallasa Liverpool."