Usmanov: Arsenal na dab da cin kofi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Alisher Usmanov ya ce nasara na ga Arsenal.

Mutum na biyu cikin masu zuba jari a kulob din Arsenal, Alisher Usmanov, ya yi amanna cewa kulob din na dab da cin kofuna a Gasar wasanni.

Kulob din na Arsenal dai ya shafe shekaru tara ba tare da samun azurfa ba, kafin ya daga kofin FA Wembley a kakar wasannin bana.

Hamshakin mai kudi dan kasar Uzbek wanda ke rike da kashi 30 cikin dari na hannun jarin kulob din, Usmanov ya ce wasu nasarori masu yawa na nan tafe ga kulob din.

Usmanov mai shekaru 60 ya ce, "Zamu fara wannan sabon karni a Arsenal, za kuma mu ci kofuna. Cin kofi shi ne abu mafi mahimmanci a harkar kwallon kafa."

Ya kuma kara da cewa, "An tsara komai tsaf domin kai wa ga samun nasara."