Xavi ya yi ritayar buga wa Spaniya wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Xavi ya fara buga wa Spaniya wasa a shekarar 2000 yana da shekaru 20

Dan wasan tsakiya na Barcelona Xavi Hernandez ya sanar da yin ritaya daga buga wa kasarsa ta Spaniya wasa.

Dan wasan mai shekaru 34 ya taimaka wa kasarsa cin gasar kofin duniya da gasar zakarun Turai biyu.

Xavi ya ci wa Spaniya kwallaye 13 a wasanni 133 da ya buga, fiye da duk wani dan wasan kasar ban da masu tsaron gida.

Ya fada wa taron manema labarai a Barcelona cewa, yana godiya game da zamansa a Spaniya a shekarun da ya kira masu kayatarwa.

An zabe shi gwarzon dan wasa a gasar zakarun Turai a shekara ta 2008, inda Spaniya ta kawo karshen jiran shekaru 44 ba tare da cin wani kofin duniya ba.