Rogers ya koyi darasi a wurin van Gaal

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rodgers ya ce zai ci gaba da sa ido domin kara daukar darussa

Kocin kulob din Liverpool Brendan Rodgers, ya ce ya koyi darasi daga salon sabon kocin Manchester United Louis van Gaal yadda yake horas da kungiyar.

Rogers, ya kuma ce a yanzu haka ya sa ido kan kocin dan kasar Netherlands, wanda ya ke abokin hamaiya a matsayinsa na kocin Manchester United.

Ya ce, "Idan ka kasance mai horas da 'yan wasa, to sai ka rinka kallon wadanda ke da hange tare da tunani, hakika van Gaal na daya daga cikin su."

Ya kuma kara da cewa, "Hakika ina daga cikin masu sha'awar yadda ya ke gudanar da aikinsa."

Rogers ya ce, " Gogaggen koci ne mai kirki wanda ya yi aiki a manyan kulob-kulob.